IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani A Kasar Kenya

22:09 - May 26, 2018
Lambar Labari: 3482695
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a birnin Nairobi na kasar Kenya.

An Gudanar Da Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani A Kasar KenyaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka saba gudanawa a kasar Keya cikin kowane watan ramadana mai alfarma a birnin Nairobi.

Ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Nairobi ne dai ya saba daukar nauyin shirya wannan gasar kur’ani a kowace shekara a cikin watan Ramadan.

A wannan karon ma gasar takebanci dalaiban makarantun firamare da sakandare ne, kuma gasar ta kunshi matakai daban-daban, kama daga bangaren hardar dukkanin kur’ani, da kuma kasa da kasa, gami da tilawa da kuma tajwidi.

A yau ne za a bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.

3717644

 

 

captcha