IQNA

Keta Alfarmar Masallacin Quds Da Yahudawa Ke Yi Na Karuwa

23:33 - May 22, 2018
Lambar Labari: 3482684
Bangaren kasa da kasa, daraktan masallacin Quds mai alfarma ya bayyana cewa cin zarafi da keta alfarmar masallacin quds da yahudawa ke yi na ci gaba da karuwa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sheikh Umar Kiswani daraktan masallacin Quds mai alfarma ya bayyana cewa keta alrmar masallacin quds da yahudawa ke yi na ci gaba da karuwa tun bayan da Trump ya mayar da ofishin jakadancin Aurka zuwa binin Quds.

Malamin ya ce ko shakka babu abin da ya faru na mayar da wannan ofishi da uma amincewa da birnin Quds a matsayin babbar birnin haramtacciyar kasar Ira’ila da Amurka ta yi babban cin zarafi ne ga dukkanin musulmi na duniya baki daya.

Ya ce wannan abin da Amurka ta yi yana a matsayin bayar da lasisi ne ga yahudawa da su ci gaba da cin karensu babu babbaka a kan muuslmin palastinu.

Ya kirayi musulmi da larabawa masu sauran lamiri, da su ci gaba da dauka dukkanin matakan da suka dace domin tunkarar wannan cin zarafi da keta alfarmar wannan masallaci da birni mai albarka.

3716395

 

 

captcha