IQNA

Shiri Mai taken Sanin Kur'ani Da Imam Hossain (AS) A Richmond Canada

22:48 - February 17, 2018
Lambar Labari: 3482404
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azzahra a garin Richmond na kasar Canada za ta gudanar da wani shiri mai taken kur'ani da Imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin muslimlink.ca cewa, a ranar 25 ga watan Maris mai kamwa ne za a gudanar da wannans hiri tare da halartar musulmi.

Wannans hiri dai zai kunshi bayanai da kuma baje koli na kayayyakin musulunci da suka hada da littafai, da kuma kayan fasaha, gami da wasu daga cikin alluna masu dauke da bayani kan a cikin hoto.

Baya ga haka kuma za a nuna wasu daga nauin kayan abinci na Halal da musulmi suke yin amfani da su musamman a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma.

Alkur'ani mai tsarki dai yana a matsayin littafin dukkanin musulmi baki daya, yayin da kuma sunnar manzon Allah take a matsayin mai fassara shi, kamar yadda kuma za a nuna wasu daga cikin kayan ashura a wurin bajen kolin.

3692362

 

captcha