Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake mayar da martani a yau kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Syria, Qasemi ya bayyana cewa har kullum Isra’ila tana son ta rika wawantar da al’ummomin duniya kan ta’addancinta a kan kasashen musulmi.
Ya ce Syria tana hakkin ta yi amfani da karfinta domin kare kasarta daga duk wani shishigi da wani zai iya yi mata, kamar yadda dokokin kasa da kasa sun amince da hakan, kuma kakkabo jirgin Isra’ila da ya kai hari a Syria hakan yana bisa ka’ida, bai sabawa ko daya daga cikin dokokin majalisar dinkin duniya.
Dangane da babatun da Isra’ila da wasu daga cikin kasashen da ke mara mata baya a yankin suke na cewa Iran tana shiga cikin harkokin Syria, Qasemi y ace Iran ta shiga a Syria ne bisa gayyatar halastacciyar gwamnatin Syria, kuma Iran tana baiwa gwamnatin Syria shawarwari kan dubarun yaki domin kare kasarta, wannan kuma ana yi a ko’ina cikin duniya.