Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a yau daruruwan jama'a ne suka gudanar da gangami a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon domin nuan rashin amincewa da kudirin Trump na mayar da birnin Quds fadar mulkin yahudawa.
Bayanin ya ce masu gangamin sun yi ta rera taken nuna rashin amincewarsu da kudirin na Trump, tare da jaddada cewa Quds mallakin musulmi da larabawa ne.
Jami'an tsaron Lebanon sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar, bayan da wasu suka fara jifar ginin ofishin jakadancin na Amurka da duwatsu.