IQNA

Martanin Azhar A Kan Kudirin Trump

21:37 - December 10, 2017
Lambar Labari: 3482186
Bangaren kasa da kasa, babban malamin cibiyar Azhar ya mayar da martini a kan kudirin Trump dangane da birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azhar ya mayar da martini a kan kudirin Trump dangane da birnin Quds na mayar da shi babban birnin Isra'ila.

Shehin malamin jami'ar Al-Azhar na kasar Masar, Ahmed al-Tayeb, ya soke ganawarsa da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, a matstayin maida martani kan matakin Trump na ayyana Qudus babban birnin Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da Ahmed al-Tayeb ya fitar ya ce ya yi watsi da bukatar ta Mista Pence wanda aka tsara zasu ganawa a wata ziyara a kasar ta Masar a ranar 20 ga watan nan 

Babban limamin na Al-Azhar, ya yi tir da allawadai da kakkausar murya dangane da matakin shugaba Trump na mayar da ofishin jakadamcin Amurka zuwa Qudus da kuma ayyanasa a mastayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.

Sanarwar da Al'Azhar ta fitar ta ce a makon da ya gabata ne Amurka ta aike mata da bukatar neman ganawar mataimakin shugaban kasar Mike Pence da babban Limanin kuma ta amince, amma biyo bayan matakin Amurka marar adalci kan birnin Qudus ta soke ganawar.

Haka nan kuma malamin ya kira da a gudnar da zaman a kasashen musulmi cikin gagagwa dangane da wannan batu mai matukar hadari.

3671179

 

 

captcha