IQNA

Baje Kolin Hotunan Makka A Brooklyn

23:25 - December 08, 2017
Lambar Labari: 3482181
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje kolin hotunan birnin Makka mai alfarma a yankin Brooklyn da ke gundumar New York a Amurka.

Baje Kolin Hotunan Makka A BrooklynKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bkreader cewa, an fara gudanar da wannan baje olin ne a ckin wannan mako, kuma zai I gaba da gudana har zuwa cikin watan Afirilun 2018 mai kamawa.

Wannan baje an bude shi ne tare da baje hotunan birnin Makka mai alfarma, da suka hada da hotunan na fina-finan bidiyo wadanda ae nunawa a wurin.

Babbar manufar baje kolin dai ita ce kara bayyana matsayin wurare masu tsarki na musulmi, musamman bnin Makka wanda a nan ka’abah take wadda ita ce alkiblar musulmi baki daya.

Bae kolin Brooklyn yana a matsayin wani babban ci gaba ga musulmi, ta yadda za su iya yin amfani da wannan damar yin bayani ga wasu wadanda ba musulmi ba kan Ka’aba da kuma matsayinta a wurin musulmi da kuma addinin muslunci.

3670190

 

 

 

captcha