IQNA

Kamfen Yaki Da Nuna Kyamar Musulmi A London

23:00 - October 17, 2017
Lambar Labari: 3482010
Bangaren kasa da kasa, musulmin birnin London sun fito da wani kamfe na nuna kin amincewa da kyamar msuulmi a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Standard cewa, wata kungiyar musulmi tare da hadin gwiwa da jami'an tsaro da kuma kamfanonin jigilar jama'a sun bullo da hanyar yaki da kyamar msuulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, babbar manufar hakan ita ce kawo karshe ko rage yawan samun matsalolin kyamar msuulmi da ake yia cikin birnin London a cikin lokutan baya-bayan nan.

Sau da yawa akan samu irin wadannan matsaloli ne a wuraren hawan ababen hawa kamar jiragen kasa ko kuma motocin bas, inda akan yi wa msuulmin izgili da cin zarafinsu, musamman ma matan musulmi, wadan da suke sanye da lullubi.

Jami’an tsaron kasar Birtaniya suna daukar kwararan matakai wajen ganin sun shiga kafar wando daya da masu cin zarain musulmi saboda addininsu.

Yama musulmi ta karu ne a kasar Birtaniya sakamakon ayyukan ta’addanci da kungiyoyin wahabiyawa ‘yan takfiriyya suke aikatawa akasar da ma wasu kasshen turai, wadanda suke samun goyon baya daga gwamnatin wahabiyawa ta Al saud da kuma makudan kudade.

3653708


captcha