IQNA

Dan Majalisar Australia Ya Caccaki Donald Trump Kan Hana Musulmi Shiga Amurka

23:25 - October 16, 2017
Lambar Labari: 3482005
Bangaren kasa da kasa, Ed Husic dan majalisar dokokin kasar Australia ya yi kakakusar suka kan dokar Trump ta hana musulmi daga wasu kasashe shiga Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar SBS cewa, Ed Husic ya bayyana hakan nee a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Astralia.

Inda ya ce Trump ya hana musulmi daga wasu kasashe shiga Amurka ne saboda addininsu, inda dan majalisar ya ce wannan babban abin kunya ne ga kasar Amurka wanda bata taba ganin irinsa ba a lokacin Trump, domin Amurka ta suna wajen fadin dimukradiyya da kare hakkokin dan adam da girmama akidarsa, sabanin mulin Trump.

Ya kara da cewa, tun daga shkara ta 2005 yana zuwa Amurka a kowace sekara, amma sakamakon wannan doka ta kiyayya ga msuulmi da gwamnatin Trump ta kafa, zai sake yin nazari kan ko zai sake zuwa Amurka, domin kuwa a yanzu ba Amurka ce ta dimukradiyya ba.

Ya ce babban abin da yasa zai sauya ra’ayinsa kan zuwa Amurka shi ne, shi mutum ne mai girmama dan adam, kuma ba zai iya ganin ana wulakanta wasu agabansa saboda addinsu ba kuma ya yi shiru, saboda haka daina zuwa Amurka shine yafi a gare shi.

3653401


captcha