IQNA

Makamai Masu Linzami Ne Amsa Ga Duk Wani Wawancin Trump

23:12 - October 08, 2017
Lambar Labari: 3481981
Bangaren siyasa, Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya bayyana cewa dakarunsa za su dauki sojojin Amurka tamkar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh matukar dai Amurka ta sanya takunkumi da bata sunan dakarun nasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari yayi wannan jan kunnen ne a yau din nan Lahadi a daidai lokacin da rahotanni suke cewa shugaban Amurka Donald Trump na shirin sanar da wasu sabbin matakai a kan Iran ciki kuwa har da wasu sabbin takunkumi da kuma sanya Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) cikin kungiyoyin ta'addanci.

Janar Jafari ya ce kamar yadda a baya muka sanar cewa matukar dai Amurka ta sanya wasu sabbin takunkumi, to kuwa sai dai Amurkawa su matsar da sansanonin sojojinsu da suke yankin nan zuwa wasu wajaje masu nisan sama da kilomita 2000, wato zangon da makamai masu linzami na Iran za su iya ci.

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sake jaddada aniyar dakarun nasa da sauran dakarun Iran na ci gaba da shirin makamansu masu linzami da nufin kare kasar Iran daga duk wata barazana ta makiya, yana mai jaddada cewa matukar Amurka ta aikata barazanar da take yi na aiwatar da dokar CAATSA da zai ba da damar sake kakaba wa Iran takunkumin, hakan yana a matsayin ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya kenan wanda Iran kuma za ta mayar da martani kan hakan.

3650286


captcha